Home Labaru Sulhu: Yan Sanda Sun Saki Yan Arewa 123 Da Aka Hana...

Sulhu: Yan Sanda Sun Saki Yan Arewa 123 Da Aka Hana Shiga Legas

484
0

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Legas ta saki ‘yan Arewacin Najeriya 123 da aka tsare aka hana shiga jihar.

DSP Bala Elkana Kakakin rundunar ‘yan sanda na Legas

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, DSP Bala Elkana, ya ce bayan gudanar da bincike a kansu, babu wani abun laifi da aka samu tattare da su.

Ya ce an yi zarginsu ne saboda yadda suka shigo cikin Legas cike da motaci dauke da Babura, amma daga bayan, an gane yawancinsu mazauna Legas ne da suka tafi gida Sallar Layya.

Haka zalika shugaban rundunar yan banga, a jihar Legas,  Yinka Egbeyemi, ya ce an kama su ne domin tabbatar da tsaron jihar daga yan baranda.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da labarin tsare su, a shafinta na Tuwita.