Tsaro: Gwamnan Zamfara Ya Tsige Sarakunan Gargajiya

  714
  0
  Bello Matawalle
  Bello Matawalle

  Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya rattaba hannu kan tsige sarkin Maru, Abubakar Cika, da kuma hakimin Kanoma, Lawal Ahmad, bisa zargin su da taimakawa ‘yan bindigan da suka kashe daruruwan jama’a.

  Karanta Wannan: Zargin Zamba: Hukumar EFCC Ta Sake Kama Makusantan Atiku Abubakar Biyu

  Gwamnatin jihar Zamfara ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin tsohon shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Abubakar domin gudanar da bincike kan alakar sarakunan da barayin.

  Rahottanni sun ce kwamitin ya samu sarakunan da gazawa, sannan kuma ya bayar da shawarar tsige su daga kujersru.

  ‘Yan bindiga dai sun kwashe wata da watanni suna kai hare-jare a jihar zamfara, abinda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a  jihar.

  A cikin watan yunin da ya gabata ne, aka dakatar da sarakunan gargajiyar bayan zanga-zangar da jama’arsu suka gudanar domin nuna bacin ransu kan yadda sarakunan ke hada kai da ‘yan bindigan masu kashe mutane.