Home Labaru Shugaban Guinea Ya Yi Bikin Sallah A Jihar Katsina

Shugaban Guinea Ya Yi Bikin Sallah A Jihar Katsina

381
0
Shugaban Guinea Ya Yi Bikin Sallah A Jihar Katsina
Shugaban Guinea Ya Yi Bikin Sallah A Jihar Katsina

Shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya yi bikin sallar layya tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura da ke jihar Katsina.

Kazalika shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya kalli hawan Durbur da majalisar masarautar Daura za ta gudanar, yayinda kuma za a nada masa rawani.

Rahotanni sun tabbatar da cewar da misalin karfe 5:20 na yamma agogon Najeriya ne, shugaban kasar Guinea, Alpha Conde ya isa Daura a jirgi mai saukar ungulu, inda ya samu kyakkyawar tarba daga shugaban kasa Buhari da kuma sarkin Daura, Umar Farouk.