Home Labaru Barka Da Sallah: An Bukaci Al’ummar Musulmi Su Kaunaci Juna

Barka Da Sallah: An Bukaci Al’ummar Musulmi Su Kaunaci Juna

385
0
Barka Da Sallah
Barka Da Sallah

An bukaci al’ummar musulmi su zama masu kaunar juna tare da rikon gaskiya da amana.

Karanta,Wannan: Sauyin Sheka: Sama Da Mutane 6000 Sun Bar Jam’iyyar APC Zuwa PDP A Jihar Zamfarahttps://i1.wp.com/hausa.libertytvradio.com/wp-content/uploads/2019/08/Matawalle.jpeg?fit=1920%2C1080&ssl=1

Kansilan Barnawa Bello Musa Mato, yi kiran a sakon sa na fatan alheri da kuma barka da Sallah ga al’ummar musulmi dake Barnawa a karamar hukumar Kaduna ta kudu da Najeriya baki daya.

Bello Musa Mato, ya ce irin wannan lokaci na bukukuwan Sallah lokaci ne da ya kamata a yawaita addu’in samun zaman lafiya da cikakken tsaro musamman kan matsalolin rashin tsaro da ake fuskanata  a yankin Arewa maso gabas da wasu jihohin arewa maso yamma.

Ya yi kira ga iyaye su sa ido a kan harkokin ‘ya’yan su domin kare su daga fadawa hannun miyagun mutane ko kuma aikata miyagun ayyuka, sai kuma ya yi kira ga masu ababen hawa su guji tukin ganganci ta la’akari da cewa za’ a samu yawan kara kainar al’umma dake gudanar da bukuwan Sallah. Daga karshe ya yi Addu’ar Allah ya ba kasramu Najeriya dauwamammen zaman lafiya da cikakken tsaro, tare da fatar ganin an yi bukukuwan Sallah lafiya an kuma kammala lami lafiya.