Home Labarai Tsaro: Dakarun Sojojin 196 Sun Ajiye Aiki

Tsaro: Dakarun Sojojin 196 Sun Ajiye Aiki

28
0
Troops Zamfara
Troops Zamfara

      
Aƙalla sojojin Najeriya 195 sun mika takardun ajiye aiki domin
ƙashin kansu ga Rundunar Sojin Najeriya.


Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya ba ta bayyana dalilin ajiyeaikin sojojin ba.

amma wasu majiyoyi sun danganta lamarin darashin ƙwarin gwiwa a tsakanin sojoji, sakamon matsin rayuwa a
ƙasar.


Mai magana da yawun rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce Babban Hafsan Sojin rundunar ya amince da
aniyar sojojin ta barin aiki domin ƙashin kansu.


Nwachukwu ya ce sojojin sun bi ka’ida kuma dokar aikin soji ta tanadi hakan, don haka, za su fara hutun barin aiki daga ranar 1
zuwa 24 ga watan Nuwamba, 2024.


Sanarwar da Birgediya-Janar O.H. Musa ya sanya wa hannu ta ce murabus ɗin sojojin zai fara aiki ne daga ranar 30 ga watan na
Nuwamba.


Nwachukwu ya bayyana cewa rundunar ta yanke tattara jerin sojojin 195 da za su bar aiki don ƙashin kansu domin sallamar su
a lokaci guda ne saboda ta yi musu kyakkyawan tsari kamar yadda ta saba a tsawon shekaru.

Leave a Reply