Home Labarai Haraji: Atiku Abubakar Ya Caccaki Matakin Gwamnatin Tarayya

Haraji: Atiku Abubakar Ya Caccaki Matakin Gwamnatin Tarayya

29
0
Atiku Abubakar
Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya koka kan
shirin da gwamnatin tarayya ta yi na kara kudin harajin harajin
VAT.


Atiku ya bayyana hakane cikin wani shirin siyasa na gidan talabijin na Channels dake Abuja, Taiwo Oyedele.

Shugaban kwamitin kan kasafin kudi da gyaran haraji Taiwo Oyedele ya ce kwamitin na gabatar
da wata doka ga Majalisar Dokoki ta kasa don kara haraji daga kashi 7.5% zuwa 10%.


Ya ce dokar da zamu gabatar wa majalisar dokokin kasar mai da harajin VAT kashi 7.5% ya koma kashi 10 cikin 100 daga shekarar 2025. Ba mu san ko yaushe za su iya zartar da dokar ba.


Amma da yake mayar da martani a cikin wata sanarwa da ya fitar  Atiku ya ce matakin dai ya biyo bayan karin farashin man fetur da kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPCL) ya yi ya kara matsalar tsadar rayuwa a cikin al’umma da kuma kara tabarbarewar ci gaban tattalin arzikin kasar.

Leave a Reply