A safiyar Talatar nan ce Hukumar Ƙwallon Kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da naɗa Bruno Labbadia a matsayin sabon kocin babban kungiyar kwalon kafa ta Najeriya Super Eagles.
Sakataren Hukumar ta NFF, Mohammed Sanusi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, Kwamitin NFF ya amince da naɗa Mista Labbadia a matsayin sabon kocin na Super Eagles.
Labbadia da zai zama kocin tawagar Super Eagles na 37, an haife shi ne a garin Darmstadt a ƙasar Jamus, a ranar 8 ga watan Fabrairun 1966.
Tsohon ɗan ƙwallo ne wanda ya taka leda a ƙungiyoyin Darmstadt 98 da Hamburger SV da FC Kaiserslautern da Bayern Munich da FC Cologne da Werder Bremen da Armenia Bielefeld da Karlsruher SC,
sannan ya taɓa lashe kofin Bundesliga da ƙungiyar Bayern Munich yana ɗan kwallo a 1994.
Ya horar da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa irin su Hertha Berlin da VfB Stuttgart da VfL Wolfsburg da Hamburger SV da kuma Bayer Leverkusen da sauran su.
Ya zama ɗan Jamus na shida ke nan da zai ja ragamar tawagar ta Super Eagles bayan Karl-Heinz Marotzke, wanda ya horar da tawagar sau biyu tsakanin 1970 da 1974, da Gottlieb Göller 1981, da Manfred Höner 1988-1989, da Berti Vogts 2007-2008 da kuma Gernot Rohr 2016-2021.














































