Home Labaru Tsaro: Dakarun Sojin Saman Nijeriya Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga A Zamfara...

Tsaro: Dakarun Sojin Saman Nijeriya Sun Yi Wa ‘Yan Bindiga A Zamfara Ruwan Wuta

916
0

Rundunar sojin sama ta Nijeriya ta ce dakarun ta sun kashe ‘yan bindiga da dama a jihar Zamfara, sakamakon  wani luguden wuta da suka yi wa sansanin ‘yan ta’addan da ke kusa da kauyen Dangote.

Daraktar yada labarai na rundunar Ibikunle Daramola ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talatar da ta gabata, inda ya kara da cewa dakarun sun kai harin ne da duku-dukun safiyar ranar ranar Lahadin, sakamakon  bayanan sirri da su ka samu.

Daramola ya ce rahotannin sun tabbatar masu da cewa, ‘yan bindigar sun tattaru a sansanin su ne ka kusa da kauyen Dangoite domin gudanar da taro a kan yadda za su kai wasu hare-hare a kauyukan da ke makwabtaka da sansanin.

A karshe Daramola ya ce, da jin wannan labara ne sai jirgin Alpha Jet ya yi wa ‘yan ta’addan  ruwan wuta tare da kashe ‘yan su da dama da kuma lalata sansanin su.

Leave a Reply