Home Labaru Ilimi Ilimi: Gwamnatin Kebbi Ta Ce A Ba Dalibai 7,000 Damar Rubuta Jarabawa...

Ilimi: Gwamnatin Kebbi Ta Ce A Ba Dalibai 7,000 Damar Rubuta Jarabawa A Kwalejin Kimiyya

437
0

Gwamnatin jihar Kebbi ta roki hukumar Kwalejin kimiyya da fasaha ta Umaru Waziri da ke jihar ta janye matakin hana dalibai dubu bakwai rubuta jarabawar zangon karatu bisa gazawar gwamnati wajen dai-dai-ta biyan kudin makarantar daliban.

Babban Sakataren hukumar kula da ilimin gaba da manyan makarantu Isah Sama, ya ce matakin da Kwalejin ta dauka ya nuna an kasa cimma dai-dai-to a tsakanin gwamnati da hukumomin makarantar.

Sama ya ce, sun yi matukar mamaki da suka ji hukumomin makarantar sun hana sabbi da tsoffi dalibai rubuta jarabawar zangon shekara ta 2018 da 2019 saboda rashin biyan kudin makaranta.

Ya ci gaba da cewa duk da matakin tattaunawa da sulhu da suka yi a tsakanin su da hukumomin makarantar, amma sai ga shi hukumar makarantar ta dauki matakin dakatar da daliban.

Sai dai shugaban makarantar Sani Aliyu,ya musanta cewa an hana daliban rubuta jarabawar, illa ya ce kamar yadda ya ke a tsarin jarabawar JAMB, idan sabbin daliban da aka ba su gurbin shiga makaranta ba su biya kudin makaranta ba, ana dauka cewa ba su da bukatar makarantar ne.

Leave a Reply