Home Labaru Biafra: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Fasto Na Cocin Angalika A Jihar...

Biafra: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Fasto Na Cocin Angalika A Jihar Imo

13
0

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne, sun kashe wani faston Cocin Angalika Emeka Merenu, wanda ya fito daga kauyen Amorji Agbomiri da ke karamar hukumar Nkwerre ta jihar Imo.

Kisan Limamin Cocin dai ya zo ne a daidai lokacin da al’ummar yankin ke kira da a yi saurin yi wa tufkar hanci, tun kafin yawan farmaki da kashe-kashen da ke faruwa su fi karfin al’ummar yankin.

Bayanai sun ce, Limamin Cocin ya hadu da ajalin sa ne sakamakon neman kariya daga sojoji, domin sama wa daliban makarantar sakandare da ke karkashin Cocin sa kariya su rubuta jarrabawar sakandare.