Home Labaru Tsaro: Babu Wani Yankin Nijeriya Da Ke Karkashin Ikon ‘Yan Ta’adda –...

Tsaro: Babu Wani Yankin Nijeriya Da Ke Karkashin Ikon ‘Yan Ta’adda – Buratai

251
0
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya
Janar Tukur Buratai, Shugaban Dakarun Sojin Nijeriya

Shugaban rundunar sojin Nijeriya Lafatanar Janar Tukur Buratai, ya ce hukumar soji ta musanta zargin cewa ‘yan ta’addan Boko Haram da kungiyar ISWAP sun mamaye kowane yanki na Nijeriya.

Buratai ya bayyana cewa, tura dakarun sojin da aka yi domin ayyukan cikin gida goyon baya ne ga ‘yan sanda a matsayin ta na hukumar tsaro da ke kan gaba.

Yayin da ya ke jawabi a wajen wani taro da kungiyar NEPAD tare da cibiyar rundunar su ka shirya a Abuja, Buratai ya ce rundunar soji ta bayyana muhimman ci-gaba da aka samu wajen kare rayuka da dukiyoyi, musamman a yankin Arewa maso gabashin Nijeriya, inda ta yi musun cewa ‘yan ta’addan sun kafa sansani.

 Matsayar Buratai dai ta bambanta da ta gwamnan jihar Born, Babagana Zullum da wasu kauyuka na jihar, wadanda su ka soki dabarun rundunar sojin Nijeriya na kafa manyan sansanoni, lamarin da ya sa su ka cire tsammani da rundunar sojin.

Rundunar sojin ta kuma yi watsi da ikirarin, inda ta ce ta ‘yantar da kananan hukumomi 22 na jihar Borno tun a shekara ta 2015.