Home Labaru Tsarin Kashe Kudi: Duk Ma’aikacin Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Ba...

Tsarin Kashe Kudi: Duk Ma’aikacin Da Ba Ya Cikin Tsarin IPPIS Ba Zai Sake Samun Albashi Ba – Zainab

907
0
Zainab Ahmed, Ministar Kudi
Zainab Ahmed, Ministar Kudi

Ministar kudi Zainab Shamsuna Ahmad, ta ce duk ma’aikacin gwamnatin tarayya da baya cikin tsarin biyan albashi na bai-daya ba zai sake samun albashin sa ba.

Zainab Ahmad ta bayyana haka ne, yayin da ta gabatar da jawabi game da tsare-tsaren kashe kudi na gwamnatin tarayya na matsakaici zango a Abuja, inda ta ce dokar za ta fara aiki ne daga watan Oktoba.

Ministar ta ce, wannan mataki ya zama wajibi, domin toshe duk wasu ramuka da kudaden gwamnati ke bi su na bacewa, tare da kokarin rage kudaden ayyukan yau da kullum da gwamnati ke kashewa.

Ta ce kudaden da ake kashewa a kan ma’aikata da ‘yan fansho sun haura naira tirilyan 3 kuma kara hauhawa su ke yi, amma gwamnati na daukar mataki a kai, inda shugaban kasa ya bada umurnin cewa daga watan Oktoba na shekara ta 2019, dukma’aikatu da hukumomi su tabbatar sun shigar da ma’aikatan su a tsarin albashi na bai-daya.