Rukunin ‘yan Nijeriya na farko da ya kunshi mutane 84 sun iso Nijeriya daga kasar Afirka ta kudu, inda su ka sauka a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
Jami’in ma’aikatar kasashen waje ta Nijeriya ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja, inda ya ce duk da cewa ‘yan Nijeriya 313 aka tabbatar za a dauko, amma mutane 84 daga cikin su kadai aka iya tantancewa.
Wani ma’aikatar harkokin wajen Nijeriya ta bayyana cewa, ‘yan Nijeriya 640 ne su ka bayyana niyyar su ta dawowa gida, kuma tuni sun yi rajista su na shirin tantancewa kafin a fara jigilar su, sannan rukuni na biyu za su dawo Nijeriya a ranar Juma’a mai zuwa.
Jami’in ya kara da cewa, ya kamata a ce jirgin Air Peace da zai dauko mutanen ya taso tun da misalign karfe 9 na safe, amma hakan bai yiwu ba saboda bincike da tsare-tsaren da jami’an hukumar shige da fice su ka gudanar a kan su, sannan an samu tsaiko a na’urar komfuta, don haka mutane 84 kadai aka iya daukowa saboda duk mintin da jirgin ya kara a filin jirgi zai biya karin kudin wurin tsayawa.