Home Labaru Tsaro: An Horar Da ‘Yan Kato Da Gora A Shiyar Arewa Maso...

Tsaro: An Horar Da ‘Yan Kato Da Gora A Shiyar Arewa Maso Gabashin Najeriya

307
0

Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada horo na musamman ga ‘yan kato da gora a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Kungiyar ‘yan kato da gora da kuma yan banga wadanda suka fito daga jihohin Borno, Adamawa da kuma Yobe, ne suka sami horon yadda za su taimakawa kokarin gwamnati wajen yaki da Boko Haram.
Cibiyar a karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ta horar da matasan akan shugabanci da zama Jakadu na gari , inda aka bukaci ce su, su yi amfani da abinda suka koya domin samar da zaman lafiya.
Darakta janar na cibiyar, Mr Jonah Bawa, ya ce sun horar da matasan ne kan yadda za su yi mu’amula da mutane da sauya tunaninsu, don taimaka wa kasarsu.
Wani jami’in kungiyar Civilian JTF na jihar Borno, Abba Aji, ya ce gwamnati za ta ci gaba da kula da wadanda suka sadaukar da rayukansu wajen samar da tsaro a jihar.
Shi ma wakilin majalisar dinkin duniya a Najeriya, Mista Mathew Alao, ya yi fatan wadanda suka sami horon za su yi amfani da abinda suka koya wajen sasanta al’umma da inganta tattalin arzikin kasa.