Home Labaru Yabo: Ba Abin Da Buhari Ya Fi Ba Muhimmanci Irin Inganta Jin...

Yabo: Ba Abin Da Buhari Ya Fi Ba Muhimmanci Irin Inganta Jin Dadin Al’umma – Osinbajo

353
0
Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinku-, Osinbajo
Mafi Karancin Albashi: Kungiyar Kwadago Ta Kwantar Da Hankalinku-, Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jaddada manufar shugaba Muhammadu Buhari ta bada fifiko a bangaren inganta jin dadin rayuwar al’umma.

Osinbajo, ya ce nasarorin gwamnatin shugaba Buhari musamman a bangaren shirye-shiryen bada tallafi, manuniya ce ta yadda ya ba bangaren inganta jin dadin al’umma mahimmanci.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana haka ne, yayin kaddamar da wasu kananan masana’antu na man gyada da sabulu, baya ga aikin samar da wutar lantarki a yankunan karkara da gwamnatin jihar Bauchi ta aiwatar.

Ya ce shugaba Buhari zai ci-gaba da dawwama kuma ba zai gushe ba wajen bada fifiko a fagen inganta jin dadin rayuwar al’umma na.

Bayan isar sa Bauchi, mataimakin shugaban kasa ya garzaya karamar hukumar Ningi, inda ya kaddamar da katafaren aikin samar da wutar lantarki musamman ga yankunan karkara na jihar.

Leave a Reply