Home Labaru Tsaro: Abinda Ya Sa Muke Neman Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Adamu

Tsaro: Abinda Ya Sa Muke Neman Sulhu Da ‘Yan Bindiga – Adamu

338
0
Mohammed Adamu, Shugaban Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban rundunar ‘yan sandan Najeriya Mohammed Abubakar Adamu, ya ce sulhu tsakanin jami’an ‘yan sanda da ‘yan bindiga da wasu gwamnonin jihohin arewacin Najeriya suka fara yi abu ne mai kyau wanda zai kawo zaman lafiya.

Adamu, ya ce an sami saukin ayyukan ‘yan bindiga da kuma masu garkuwa mutune idan aka yi la’akari da yadda abubuwan ke aukuwa a watannin baya.

Shugaban rundunar, ya bayanna hakan ne a zantawarsa da manema labarai jim kadan bayan kammala tattaunawar shugabannin hukumomin tsaro da shugaban kasa Buhari, inda ya  ce marigayi Shugaba Umaru Yar’Adua ya yi amfani da irin wannan hanya ta sulhu domin magance matsalar ‘yan Neja-Delta.

Ya ce a wancan lokacin da gwamnati ta tsaya ta yi nazarin cewa ba yaki bane zai magance matsalar ya zama dole ayi sulhu, saboda haka  dubarun yaki ba lallai sai an dauki makamai ba, akwai hanyoyin neman sulhu wadda a lokuta da dama tafi samar da zaman lafiya.Daga karshe, ya kara da cewar bai zai zama wajibi ba, ace dole sai an kama yan bindiga, za a iya amfani da hanyar sulhu domin dakatar da matsalar gaba daya.

Leave a Reply