Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Najeriya Na Maraba Da Masu Zuba Jari – Buhari

Tattalin Arziki: Najeriya Na Maraba Da Masu Zuba Jari – Buhari

520
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Najeriya na maraba da masu son saka hannun jari a fannin ayyuka musamman na samar da wutar lantarki da zai inganta kasuwanci.

Shugaban kasa ya bayanna haka a lokacin da yake jawabi a yayin ganawarsa da jakadar kasar Jamus a Najeriya, Birgitt Ory, inda ta ce gwamnati ba za ta saba yarjejeniyar kwangilar ba idan kamfanonin Jamus suna sha’awar sa hannun jari a Najeriya.

Mai magana da yawun shugaban kasa Femi Adesina, ya ce shugaban kasa ya ce ‘yan Najeriya sunyi maraba da kwangilar da aka rattabu hannu kai tare da kamfanin Siemens na Jamus inda ya ke fatan kasashen biyu za su amfana da kwangilar.

Ya ce Najeriya na godiya bisa taimakon da Jamus ke ba ‘yan Najeriya a matsayin tallafi na mutanen da suka rasa muhallansu a yankin Arewa maso Gabas da ziyarar da shugaban Jamus, Angela Merkel ta kai Najeriya a watan Augustan 2018 na kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu.

Itama ana ta jawabin jakadar kasar Jamus a Najeriya, Birgitt Ory ta ce ta yi matukar farin cikin samun daman yin aiki a Najeriya duba da cewa ta dade tana burin afkuwar hakan.