Home Labaru Tallafi: Bankin CBN Ta Ware Naira Biliyan 30 Domin Habbaka Noman Kwakwan...

Tallafi: Bankin CBN Ta Ware Naira Biliyan 30 Domin Habbaka Noman Kwakwan Manja A Najeriya

328
0
Babban bankin Nijeriya
Babban bankin Nijeriya

Babban bankin Najeriya, CBN ta bayyana cewa ta ware kimanin kudi naira biliyan 30 domin habbaka noma kwakwan manja a Najeriya.

Godwin Emefiele, Gwamnan Babban Bankin Najeriya

Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da wasu gwamnoni a Abuja, inda ya ce sun raba kudaden ne ga wasu kamfanoni guda 6 ta hannun bankuna.

Daga cikin kamfanonin da suka samu wannan tallafi domin fadada noman kwakwan manja akwai PZ Wimar, da Biase Oile company Ltd, da kuma Eyop, Okomu Oil company, da  Presco Oil Company da kuma Siat LTD.

Emefiele,  ya kara da cewa suna jiran kamfanin Ada Palm na jahar Imo ta mika kokon barar ta, inda ya bayyana cewa Najeriya na bukatar tan miliyan 2  na manja a shekara, amma tan miliyan 1 kadai ake iya samarwa, wanda hakan ya samar da gibin tan miliyan 1 da ake bukata. Ya ce muddin ana son cike wannan gibin sai an noma sabbin hektocin gona 312,500 a karkashin tsarin noman zamani tare da sa ran samun tan 4 a kowanne hekta.