Home Labaru Tsarin ‘Yan Tinke: Manyan Jam’iyyu A Najeriya Sun Nuna Rashin Amincewar Su

Tsarin ‘Yan Tinke: Manyan Jam’iyyu A Najeriya Sun Nuna Rashin Amincewar Su

82
0

Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma babbar jam`iyyar hamayyar ta PDP sun bayyana rashin goyon bayan su a siyasance kan tsarin zaben fidda gwani ta hanyar ‘yar tinƙe.

A ranar Talata ne ‘yan majalisar dokoki na ƙasa suka zartar da kudurin dokar da zai tilasta wa jam`iyyun siyasa gudanar da zaben fid da gwani ta hanyar ‘yar tinƙe.

Sai dai a wata ganawa da manema labara, shugaban ƙungiyar gwamnoni na Jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya yi fatali da dokar yana mai cewa yin hakan zai sa aiki ya yi wa hukumar zaɓe ta INEC yawa.

A cewarsa, matakin ba shi da gurbi a shari’ance kuma yana cike da kalubale.

A nata ɓangaren, jam’iyyar PDP ta bakin sakatarenta na ƙasa, Sanata Ibrahim Umar Tsauri, ta ce ba ta ga wani alheri tattare da tanadin da dokar zaɓen ta yi na tilasta wa jam`iyyun siyasa bin tsarin `yar tinƙe wajen gudanar da zaɓen fid da gwani ba, musamman ma a zaɓen `yan majalisun dokokin, face dora wa `yan majalisar ɗawainiyar da babu gaira ba sabab.