Home Labaru Najeriya Na Shirin Kashe Sama Da Naira Tiriliyan 348

Najeriya Na Shirin Kashe Sama Da Naira Tiriliyan 348

95
0

Majalisar Zartarwa ta gwamnatin tarayya ta ware tsabar kudi sama da Naira tiriliyan 348 a matsayin kuɗin da za a kashe a Shirin tsarin ci gaban Ƙasa  wato Naitional Development Plan a turance.

Ministar Kuɗi da Kasafi Zainab Ahmed, ta bayyana haka jim kaɗan bayan kammala zaman da majalisar ta yi ranar Laraba, wanda mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Zainab Ahmad ta ce shirin na shekara biyar zai maye gurbin shirin tsarin farfado da tattalin arziki Economic Recovery and Growth Plan ERGP wanda zai ƙare a watan Disamban 2021.

Ta ce an tsara shirin ne zuwa aji shida da suka haɗa da haɓaka tattalin arziki da cigaba, da ayyukan raya ƙasa, da shugabancin al’umma, da taimaka wa rayuwa, da kuma ciyar da al’umma da yankuna gaba.

A cewar ta, gwamnatin tarayya za ta faɗaɗa karɓar haraji sannan ta ƙarfafa ɓangaren ‘yan kasuwa ta hanyar sama musu damarmaki da zummar samun kuɗin gudanar da shirin.

Ministar kudin tace shirin ya yi hasashen za a samu haɓakar ma’aunin tattalin arzikin Najeriya da kashi 5 cikin 100, inda hukumomin gwamnati za su samar da sama da Naira biliyan 49  yayin da ɓangaren ‘yan kasuwa zai samar da sama da Naira tiriliyan 298.