Home Labaru Kin Jinin Baki: ‘Yan Afrika Ta Kudu Dauke Da Makamai Sun Yi...

Kin Jinin Baki: ‘Yan Afrika Ta Kudu Dauke Da Makamai Sun Yi Zanga-Zangar Kyamar Baki

372
0

Akalla mutane biyu sun rasa rayukan su, yayin da jami’an tsaro su ka kama wasu da dama bayan wata zanga-zangar kin jinin baki da ‘yan kasar Afrika ta kudu dauke da muggan makamai su ka gudanar, inda su ke neman lallai baki su gaggauta barin kasar su.

Wasu kafofin labarai a kasar sun bayyana yadda aka fuskanci arangama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an ‘yan sanda, a lokacin da su ka rika kone shaguna da kadarorin baki a birnin Johammesburg.

Shugaban ‘yan sanda na kasar Afrika ta kudu David Tambe, ya ce mutane biyu sun mutu sakamakon harbin bindiga da sukar wuka, duk da dai bai bada tabbacin baki ne ko ‘yan kasar ne su ka rasa rayukan su a hargitsin ba.

David Tambe, ya ce masu zanga-zangar sun rika kone shaguna da motoci da sauran kadarorin jama’a galibi na ‘yan kasar ta Afrika ta kudu.

Yanzu haka dai akwai ‘yan Afrika ta kudu kusan dari 5 da ke hannun jami’an tsaro, bisa zargin su da farmakar baki da ke zaune a kasar, bayan da matakin ya fara haddasa wa kasar tsamin dangantaka da takwarorin ta musamman Najeriya.