Home Labaru Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene – Ngige

Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene – Ngige

290
0
Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene - Ngige
Tsarin IPPIS: Yajin Aiki Kungiyar ASUU Haramtaccene - Ngige

Ministan kwadago da ayyuka Chris Ngige ya yi karin haske a kan sabanin da gwamnatin tarayya ta samu da kungiyar Malaman jami’o’i ASUU.

Ngige ya bayyana cewa, haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ke yi, sakamakon yadda ta tursasawa ‘ya ‘yan ta shiga cikin tsarin albashin nan na IPPIS da gwamnatin Buhari ta kirkiro.

Ministan ya bayyana haka ne a fadar shugaban kasa jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa wamnda ya gudana a ranar Laraba.

Da ya ke amsa tamboyoyin manema labarai, Chris Ngige ya ce kungiyar ASUU ba ta sanar da gwamnatin tarayya halin da ta ke ciki ba, sai kurum ta tafi yajin aikin makonnni biyu.

Haka kuma, Ministan ya ce ya na daga cikin rashin gaskiya ace an biya masu yajin aiki albashi, domin kuwa babu wani aiki da su ka yi a lokacin da su ka kauracewa ofisoshin su.

Chris Ngige ya tabbatarwa  manema labarai cewa, ma’aikatar sa ta shirya zama da kungiyar ASUU a Ranar Alhamis domin shawo kan sabanin da ya shiga tsakanin su da gwamnati.