Home Labaru Martini: Jonathan Ya Karya Ta Zargin Karbar Naira Miliyan 300 A Hannun...

Martini: Jonathan Ya Karya Ta Zargin Karbar Naira Miliyan 300 A Hannun APC

266
0
Martini: Jonathan Ya Karya Ta Zargin Karbar Naira Miliyan 300 A Hannun APC
Martini: Jonathan Ya Karya Ta Zargin Karbar Naira Miliyan 300 A Hannun APC

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya musanta bayanan da ke cewa ya karbi kyautar naira miliyan 300 daga hannun jam’iyyar APC a lokacin zabe jihar Bayelsa.

Jonathan ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawun sa Ikechukwu Eze, inda ya ke maida martani ga wata kungiyar siyasa mai suna APC Reformation Forum da ta yi zargin cewa, tsohon zababben gwamnan jihar larkashin jam’iyyar APC, David Lyon y aba jonathan wadannan kudade.

Jonathan ya cigaba da cewa, wannan labari da wannan kungiya ta ke danganta shi da shi a kafafen yada labarai na zamani ba shi da tushe balle makama.

Kungiyar dai, ta zargin David Lyon ya ba jonathan wadannan kudade domin kula da bakin da ya gayyata zuwa nadin sa, batunda Jonathan ya bayyana a matsayin karya tsagwaran ta.

Haka kuma Jonathan ya shaida wa duniya cewa, babu wata mota da APC ba shi, idan kuma akwai wanda ke da masaniya game da ba shi motar sai ya fallasa takardun ta da kuma inda ta ke.

A karshe Jonathan ya ce, an gudanar da zaben jihar Bayelsa a akwatunan zabe da kuma kotuna, saboda haka lokacin ce-ce kuce ya wuce, kamata ya yi al’ummar jihar  su rungumi kaddara su jira wani lokaci a nan gaba.