Home Labaru Kasuwanci Cigaba: Dangote Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnatin Ta Samar Da Hanyoyin Habaka...

Cigaba: Dangote Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnatin Ta Samar Da Hanyoyin Habaka Tattalin Arzikin Kasa

453
0
Cigaba: Dangote Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnatin Ta Samar Da Hanyoyin Habaka Tattalin Arzikin Kasa
Cigaba: Dangote Ya Ce Akwai Bukatar Gwamnatin Ta Samar Da Hanyoyin Habaka Tattalin Arzikin Kasa

Fitaccen dan kasauwa Aliko Dangote ya ce gwamnatocin Nijeriya na baya da na yanzu ba su tabuka wani abin a zo gani wajen ciyar da tattalin arzikin kasa gaba ba, lamarin da ya sa tattalin arzikin ba ya cigaba.

Dangote ya bayyana haka ne a lokacin wani taro da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya shirya a Abuja, inda ya ce kokarin da gwamnatin Buhari ke yi na karkatar da akalar tattalin arzikin daga man fetir ya yi kadan.

Aliko Dangote ya ce, babu wasu kwararan tsare tsare da gwamnatin ta tanadar na karkatar da tattalin arzikin kasa daga man fetir, saboda haka ya bada shawarar kara kaimi wajen wasu ayyukan masu muhimmanci, musamman a wannan lokaci da farashin mai ya yi kasa.

Attajirin ya kuma shawarci gwamnatin Buhari ta kara kokari wajen maida hankali a kan karkokin r noma da bangaren masana’antu, saboda su ne su ke samar da ayyukan yi ga al’umma.