Home Labaru Tsagerun ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’An Tsaro 100 A Jihar Benue

Tsagerun ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Jami’An Tsaro 100 A Jihar Benue

17
0

Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, ya ce ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro sama da 100 a bakin aikin su cikin shekaru biyu da su ka gabata.

Samuel Ortom ya bayyana haka ne, yayin wanni taron manema labarai da ya gudana a Abuja, inda ya damuwar sa da abin da ke faruwa ta sa ya furta cewa wasu makiyaya na shigowa daga kasashen waje da shirin kwace Nijeriya.

Ya ce sama da Jami’an tsaro 100 aka hallaka a jihar Benue, a kokarin su na tabbatar da zaman lafiya a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Ortom, ya ce duk wanda yace komai na tafiya daidai a Nijeriya ba mutumin kirki ba ne, ya na mai jaddada cewa shugaba Buhari ya na da kudiri mai kyau, amma waɗanda ke zagaye da shi ne su ka kwace ragamar shugabancin Nijeriya.