Home Labaru Rashin Iya Jagorancin Ganduje Ne Silar Rikicin Apc A Kano – Shekarau

Rashin Iya Jagorancin Ganduje Ne Silar Rikicin Apc A Kano – Shekarau

75
0

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce rashin iya jagorancin jam’iyya daga gwamna Ganduje ne silar rikicin da APC ke fama da shi a jihar.

Sanata Shekarau ya bayyana wa manema labarai haka ne, jim kaɗan bayan kammala wani taro da ya yi da magoya bayan sa dangane da halin da shugabancin jam’iyyar ta APC ke ciki a jihar Kano.

Shekarau ya zargi shugaban Jam’iyyar APC na jihar Kano Abdullahi Abbas da iƙirarin cewa, APC a Kano ta Ganduje ce da mai ɗakin sa Gwaggo da kuma shi kan sa Abdullahi Abbas.

Ya ce an maida su saniyar ware a duk wasu al’amurra na Kano, tun daga batun taron jam’iyya zuwa sauran tarurruka da ba a rasa ba.

Ibrahim Shekarau, ya ce ƙorafin da su ka yi a kan rikicin da ke tsakanin su da ɓangaren Ganduje, a yanzu ya na gaban kwamitin sasanta rikicin APC na ƙasa a karkashin jagorancin Sanata Abdullahi Adamu.