Babban Hafsan rundunar sojin sama Air Marshall Isiaka Amao, ya tabbatar wa ‘yan majalisar dattawa cewa lokaci kaɗan ya rage ayyukan ta’addanci su zama tarihi a Nijeriya.
Air Marshall Amao ya bada tabbacin ne, kwanaki uku kacal bayan mayakan ISWAP sun kashe Janar na sojojin ƙasa a Askira Uba da ke jihar Borno.
Kwamitin sojin sama na majalisar dattawa, ya bukaci rundunar sojin ta ƙara ƙaimi a yakin da su ke yi, domin tabbatar da zaman lafiya a wuraren da lamarin ya shafa.
Hafsan sojin ya bayyana haka ne, yayin da ya ke kare kasafin kuɗi na shekara ta 2022 a gaban kwamitin majalisar dattawa, inda ya ce ‘yan ta’adda na shan luguden wuta ta ko ina babu kakkautawa, wanda hakan ke tilasta masu aje makamai.