Home Home Tsagaita Wuta: Rasha Da Ukraine Za Su Gana

Tsagaita Wuta: Rasha Da Ukraine Za Su Gana

19
0
Bayan kwashe kimanin wata guda ana tafka yaki tsakanin Rasha da Ukraine, gwamnatin Kyiv ta ce za a gudanar da wata tattauna a karo na biyu tsakanin ta da makwafciyar ta Moscow.

Bayan kwashe kimanin wata guda ana tafka yaki tsakanin Rasha da Ukraine, gwamnatin Kyiv ta ce za a gudanar da wata tattauna a karo na biyu tsakanin ta da makwafciyar ta Moscow.

Hakan dai na zuwa ne yayin da ake ci gaba da lalubo hanyoyin kawo karshen rikicin ta hanyar diflomasiya, kuma ana sa ran tattaunawar ta gudana a kasar Turkiyya.

A sakon da ya wallafa a shafin sa na facebook, David Arakhamia da ke zama dan siyasa a Ukraine ya ce, bayan cimma wata yarjejeniya ta kafar bidiyo, tawagar bangarorin biyu za su tattauna a karo na biyu a ranakun Litinin da Talata gaba-da-gaba a kasar Turkiyya.