Home Home Sauya Sheka: Abba Gida-Gida Ya Koma Jam’iyyar NNPP

Sauya Sheka: Abba Gida-Gida Ya Koma Jam’iyyar NNPP

76
0
Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2019, Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kano a zaben 2019, Abba Kabiru Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida, ya sanar da sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP.

Wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a ranar Lahadi a mazabar sa ta Diso da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano.

Hadimin sa na musamman, Ibrahim Adam ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Lahadi.

Haka kuma, Gidan Rediyon Freedom na Kano ya ruwaito cewa, cikin wadanda suka halarci taron sauya shekar Abba Gida-Gidan, sun hada da abokin takarar sa a zaben 2019, Kwamared Aminu Abdussalam da kuma shugaban jami’iyyar ta NNPP na Kano, Haruna Umar Doguwa.

Abba Gida-Gida wanda tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya marawa baya, ya sha kayi a hannun gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC ne a zaben 2019, wanda aka yi ta cece-kucen cike yake da magudi.

A karshen watan nan na Maris da muke ciki ne ake sa ran Sanata Kwankwaso zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa NNPP, inda zai kuma bayyana kudirin sa na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 da ke tafe