Home Home Harin Kaduna: Buhari Ya Bada Umurnin Harbe Duk Mai Dauke Da Ak47

Harin Kaduna: Buhari Ya Bada Umurnin Harbe Duk Mai Dauke Da Ak47

174
0
Sakamakon kazamin harin da ‘’yan bindiga su ka kai a kan jirgin kasa tsakanin Kaduna zuwa Abuja, shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron shugabannin hafsoshin tsaro na gaugawa domin tattaunawa a kan matsalar.

Sakamakon kazamin harin da ‘’yan bindiga su ka kai a kan jirgin kasa tsakanin Kaduna zuwa Abuja, shugaba Muhammadu Buhari ya kira taron shugabannin hafsoshin tsaro na gaugawa domin tattaunawa a kan matsalar.

Rahotanni sun ce shugaba Buhari ya bayyana bacin ran sa dangane da lamarin da ya kai ga rasa rayuka, inda ya bukaci hafsoshin tsaron su kara kaimi wajen murkushe ‘’yan bindigar da ke zafafa hare-haren su.

Buhari ya bukaci a kubutar da duk fasinjojin da aka sace, a kuma tabbatar da ganin an hukunta wadanda su ka aikata laifin, sannan ya ba hafsoshin tsaron umurnin harbe duk wanda aka gani dauke da bindiga kirar AK47 ba tare da izini ba.

Shugaban Buhari, ya ce ba zasu lamunci yadda wasu ke hana jama’a zaman lafiya ba, kuma kamar kowanne dan Nijeriya shi ma ya kadu da wannan hari, wanda shi ne irin sa na biyu da ya kaiga rasa rayuka da kuma jin raunuka.

Tuni dai mataimakin sa Yemi Osinbajo ya ziyarci birnin Kaduna domin gane wa idon sa halin da ake ciki, da kuma ziyarar fasinjojin da su ka samu raunuka sakamakon kazamin harin.

Leave a Reply