Home Labarai Tsadar Rayuwa: Gwamna Yusuf Ya Roki Tinubu Ya Sake Bude Iyakokin Nijeriya

Tsadar Rayuwa: Gwamna Yusuf Ya Roki Tinubu Ya Sake Bude Iyakokin Nijeriya

141
0

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya duba bukatar gaggawa ta batun sake bude iyakokin Nijeriya domin shigo da kayan abinci daga kasashen waje domin ragewa al’ummar Nijeriya radadin tsadar rayuwa.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, gwamnan ya roki wannan bukatar ne jim kadan bayan ya karbi bakuncin shugaban hukumar kwastam na Nijeriya, Alhaji Bashir Adewale Adeniyi a gidan gwamnati da ke Kano.

Gwamnan ya koka da halin matsin tattalin arziki da yunwa da ake fama da shi a kasar nan sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a kasar.

Leave a Reply