Home Labarai Ramadan: Gwamnatin Sokoto Ta Amince A Biya Ma’Aikata Da ‘Yan Fansho Kyautar...

Ramadan: Gwamnatin Sokoto Ta Amince A Biya Ma’Aikata Da ‘Yan Fansho Kyautar Rabin Albashi

35
0

Gwamnan jihar Sokoto Ahmed Aliyu ya amince da biyan kyautar rabin albashi ga daukacin ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho A kokarin ganin al’ummar musulmin jihar Sokoto sun fara azumin watan Ramadan na bana cikin nutsuwa da walwala,.

Wannan gagarumin karamcin, a cewar wata sanarwa da sakataren yada labarai na gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ya rabawa manema labarai, ta ce, biyan rabin albashin ga ma’aikatan jihar, an yi ne domin saukakawa ma’aikatan wajen gudanar da azumin watan Ramadan na bana cikin sauki.

Don haka, Gwamna Aliyu ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da watan Ramadan mai alfarma wajen addu’ar Allah ya kawo mana tallafi kan dimbin kalubalen da suka addabi Nijeriya.

Leave a Reply