Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma a jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya bayyana shirin raba kayan abinci ga magidanta 250,000 a cikin watan Ramadan na bana.
Shirin dai na da nufin rage radadin yunwa da kuma tabbatar da ganin magidanta a fadin jihar Zamfara sun gudanar da ibadarsu cikin nutsuwa da walwala.
A karkashin shirin wanda za a aiwatar da shi a kananan hukumomi 13 na jihar Zamfara, kowace karamar hukuma za ta karbi buhuna 17,500 na kayan abinci da suka hada da shinkafa, gero, sukari, da masara.
Amma, babban birnin jihar, karamar hukumar Gusau, za a bata buhunan kayan abinci 22,500.
A wani shiri na musamman ga marasa karfi, marayu da mata, za a raba musu buhunan shinkafa, gero, sukari, masara 10,000, domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin walwala.
Bugu da kari, za a ba wa marayu maza da mata tufafin Sallah da kuma karin Naira 2,000 kudin dinki ga kowannensu.