Home Labaru Gwamnatin Jihar Imo Ta Haramta Saida Giya A Tashoshin Mota

Gwamnatin Jihar Imo Ta Haramta Saida Giya A Tashoshin Mota

13
0

Gwamnan jihar Imo Hope Uzodinma, ya haramta saida Barasa da duk wasu nau’ukan lemu masu sa maye a tasoshin mota da ke fadin jihar.

Hope Uzodinma ya bayyana haka ne, yayin kaddamar da wata majalisa da ya kafa a Owerri, wadda za ta rika bada shawara a kan harkokin zirga-zirga.

Ya ce majalisar za ta maida hankali a kan abubuwa biyar, wadanda su ka hada da kula da tituna da samar da matafiya masu tuki a tsanake.

Haka kuma, majalisar za ta bada karfi wajen ganin an dauki matakin gaugawa bayan aukuwar hadurra, tare da samar da tituna masu nagarta a fadin jihar.