Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano PCACC, ta kai samame tare da rufe rumbunan ajiye kayan abinci biyar da ke kasuwar Dawanau a karamar hukumar Dawakin Tofa.
Hukumar ta gano rumbunan ne makare da waken suya da alkama da sauran kayan abinci.
Shugaban hukumar Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ya jagoranci kai samamen, lamarin da ya ba jami’an hukumar, damar fara bude wani rumbu mallakin Hamir Investment, wanda ke cike da dubban katan-katan na kayan abinci da suka hada taliya da sukari da sauransu.
Haka kuma, binciken da hukumar ta yi ya gano an boye kayan ne domin tsauwala wa al’umma a lokacin watan Azumin Ramadana da ke kara karatowa.
Rimin Gado ya ce hukumar za ta ci gaba da kai samame a rumbunan da ake boye kayan abinci domin jefa al’umma cikin tsaka mai wuya.
Haka kuma, Rimin Gado ya kai ziyara kasuwar Singa, inda ya tattauna da shugabannin kasuwar domin lalubo hanyar samar da sauki da al’umma














































