Home Home An Kama ’Yar Shekara 20 Da Buhu 5 Na Tabar Wiwi

An Kama ’Yar Shekara 20 Da Buhu 5 Na Tabar Wiwi

37
0

Rundunar ‘yan sandan jihar edo ta kama wata budurwa tare da saurayinta da buhuna biyar na tabar wiwi.

Jami’an ‘yan sandan sun kama budurwar da saurayinta ne a gidan da suke zama a unguwar Ologbo da ke karamar hukumar Ikpoba-Okha.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Chidi Nwabizor ya ce jami’an su sun yi nasarar kama mutanan ne bayan makwabtansu sun kawo rahoton cewa su na tara ganyen tabar wiwi a cikin gida, kuma bayana kai samame an gano buhuna biyar na tabar wiwi.

Nwabizor ya kara da cewa, rundunar ta kuma kama wasu mutane hudu bisa zarginsu da fasa wani turken sadarwa na kamfanin Airtel, da sace baturansa da kuma kudi kimanin Naira miliyan 12 a garin Benin.

Leave a Reply