Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, ta ce jami’an ta sun yi nasarar kashe gawurtattun masu garkuwa da mutane da dama, wadanda su ka addabi wasu yankunan birnin tarayya Abuja.
Kakakin rundunar ‘yan sandan ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Rundunar ‘yan sandan, ta ce daga cikin ‘yan bindigar da ta kashe har da wani gawurtaccen mai garkuwa da mutane mai suna Musa Wada.
Sanarwar ta ce, ‘yan sandan sun kwashe kusan mintina 30 su na gumurzu da ‘ran bindigar, lamarin da ya sa masu garkuwar da dama su ka ji munanan raunuka, ko da ya ke ɗan sanda guda ya jikkata.
Rundunar ta ƙara da cewa ta samu nasarar ne bayan ta kawar da wani mai garkuwa da mutane mai suna Abubakar Wada, wanda shi ne ya nuna wa jami’an ‘yan sandan maɓoyar su.
Musa Wada di shi ne ya kitsa satar mutane a wuraren da su ka haɗa da Mpape da Bwari a Abuja, da Kagarko a jihar Kaduna da kuma ƙauyen Nukun da ke jihar Nasarawa.