Home Labaru Tonon Silili: Akpabio Ya Bayyana Masu Cin Kwangilolin NDDC Bayan Barazanar NASS

Tonon Silili: Akpabio Ya Bayyana Masu Cin Kwangilolin NDDC Bayan Barazanar NASS

242
0

Ministan harkokin Neja-Delta, Godswill Akpabio, ya fito ya maidawa Majalisar wakilan tarayya martani sakamakon kalubalen da aka jefa masa.

Sanata Godswill Akpabio, a wata takarda da ya aike ya ambaci sunan Sanatoci hudu da ya ce sun karbi kwangiloli 74 daga ma’aikatar NDDC daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar wakilan ta ba ministan wa’adin kwana biyu ya fadi sunayen ‘yan majalisar da su ke samun kwangilar a ma’aikatar ta Neja-Delta.

Majalisa ta nuna cewa za ta garzaya kotu da Ministan Neja Deltan ganin wa’adin da aka ba sa ya kare ba tare da ya gabatar da sunayen ‘yan majalisar da suke samun kwangilar ba.

A karshen makon nan ne dai ministan ya turawa majalisa takarda mai kunshe da jerin Sanatocin da NDDC ta ba kwangiloli, daga ciki akwai Sanata Peter Nwaoboshi, wanda aka ba kwangiloli 43.

Takardar ta ce an ba Sanata Matthew Urhoghide, da James Manager, da kuma Sanata Sam Anyanwu kwangiloli 21 duk daga shekarar 2017 zuwa yanzu.

Amma sai dai Sanata Nwaoboshi, ya karyata wannan zargi, inda ya kira Akpabio, da rudadde.