Home Labaru Sarautar Fani Kayode: ‘Yan Sanda Sun Yi Wa Masarautar Shinkafi Zobe

Sarautar Fani Kayode: ‘Yan Sanda Sun Yi Wa Masarautar Shinkafi Zobe

215
0

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce ta tsananta tsaro a farfajiyar fadar sarkin Shinkafi, Alhaji Muhammad Makwashi don tabbatar da tsaro ga lafiyar sarkin.

Idan ba’a manta ba dai wasu masu sarauta sun kalubalanci sarkin da mazauna Shinkafi a kan sarautar da ya ba tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode.

Mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu, ya ce masarautar ta gano cewa wasu na kokarin jagorantar zanga-zanga a Shinkafi dan haka Masarautar ta bukaci kariya daga rundunar ‘yan sandan don gujewa tada tarzoma.

Ya ce sun tura jami’ai don gudanar da sintiri a Shinkafi don tabbatar da zaman lafiya bayan kwamishinan yan sandan jihar, CP Usman Nagogo, ya ja kunnen jama’a a kan daukar doka a hannun su.

SP Muhammad Shehu, ya ce Idan mutum yana da matsala da wani, akwai hanyoyin mika korafi wadanda suka hada da kotu amma ba za su amince wani ya tada musu tarzoma ba.

Ya kara da jaddada cewa, abinda yake faruwa a Shinkafi ba wai tsare sarkin aka yi ba kamar yadda ake bazawa, kariya ce aka bas hi.