Home Labaru Kalubalanta: Obono-Obla Yace Shugabannin Jam’iyyar APC Kan Su Kawai Su Ka Sani

Kalubalanta: Obono-Obla Yace Shugabannin Jam’iyyar APC Kan Su Kawai Su Ka Sani

223
0
Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP - APC
Babu Wanda Ya Sauya Sheka Zuwa PDP - APC

Tsohon shugaban kwamitin shugaban kasa kan bankado dukiyar gwamnati da ke hannun mutane, Okoi Obono-Obla, ya yi hasashen watakila jam’iyyar APC ba za ta ci zaben 2023 ba.

Cif Okoi Obono-Obla, ya ce shugabannin jam’iyyar APC sun sa son-rai a cikin al’amuran su, ya ce akwai abin damuwa game da yadda ake tafiyar da jam’iyyar mai mulki.

Obono-Obla, ya kara da cewa shekaru bakwai da kafa jam’iyyar APC a Najeriya, har yanzu babu rajistar da ke dauke da sunayen ainihin ‘ya ‘yan jam’iyyar.

A wani jawabi da ya yi a dandalin sada zumunta, tsohon hadimin shugaban kasan ya ce ya hango rugujewar APC idan har jam’iyyar ta gaza yin garambawul, ta yi gyara, ta sake shirya kan ta.

A cewar sa, idan har jam’iyyar ta APC ba ta yi hakan ba, za ta sha wahala wajen janyo hankalin ‘yan Najeriya a babban zaben shekarar 2023.