Home Labarai Tinubu zai yi wa ‘yan majalisa jawabi A bikin dimokuraɗiyya

Tinubu zai yi wa ‘yan majalisa jawabi A bikin dimokuraɗiyya

152
0
Tinubu (1)
Tinubu (1)

Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai yi wa zaman haɗin
gwiwa na majalisun dokoki na ƙasa jawabi gobe Laraba

a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 da ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya ba tare da katsewa ba.


Akawun Majalisa Sani Tambuwal ya ce shugaban kasan zai kuma ƙaddamar da wani sabon ɗakin karatu da aka gina a
farfajiyar ginin majalisar.


A sanarwar da ya bayar ya ce ana sanar da sanatoci da wakilai cewa a wani ɓangare na bikin cika shekara 25 na mulkin dimokuraɗiyya da wakilci a majalisa, za a yi zaman haɗin gwiwa tsakanin majalisar wakilai da ta dattawa

.
A ranar 29 ga watan Mayun 1999 aka rantsar da Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa zaɓaɓɓe, wanda ke nufin an
shiga jamhuriya ta huɗu a siyasar Najeriya,

kuma tun daga lokacin mulkin dimokuraɗiyya bai sake gamuwa da tangarɗa ba. Sai dai a yanzu ana bikin Ranar Dimokuraɗiyya ne ranar 12 ga
watan Yuni tun daga 2018

lokacin da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauya ranar daga 29 ga watan Mayun.

Leave a Reply