Mataimakin shugaban Najeriya, Shettima, ya yi kira ga kawayen Najeriya su hada kai domin magance matsalar ‘yan gudun hijira.
ya yi kiran ne a wani taron kaddamar da tsare-tsare na jihohi kan magance matsugunin cikin gida da za a aiwatar a jihohin Arewa guda hudu,
mataimakin shugaban kasan ya bayyana dabarun da gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta dauka wajen tunkarar kalubalen ‘yan gudun hijira a Najeriya,
inda ya ce gwamnati na ba da fifiko ga rayuwar al’ummar ta musamman a wannan mawuyacin lokaci.
Ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatin tarayya za ta himmatu wajen tabbatar da lafiyar da walwalar ‘yan gudun hijira a
Najeriya.
Shirin ya samo asali ne daga babban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ya tsara kan ƙaura Ndaga matsugunai
wanda ke da nufin taimakawa mutanen da ke gudun hijira a cikin gida su sami mafita mai ɗorewa.