Tinubu zai sake ganawa da wakilan ƙungiyar ƙwadago a ranar Alhamis domin cigaba da tattaunawa kan sabon tsarin mafi ƙrancin albashi.
Ministan Yaɗa Labarai da ayar da kan jama’a Muhammad Idris, ya sanar da manema labarai haka a fadar shugaban ƙasa a jiya Litinin,
yana mai cewa shugaban kasan zai ɗora ne kan tattaunawar da suka fara a makon da ya gabata, inda suka kasa cimma wata matsaya.
A ganawar ta su ta makaon jiyan gwamnatin tarayyar ta tsaya a kan tayin ta na farko Naira dubu 62,
suma kungiyoyin ƙwadagon suka kafe a kan Naira dubu 250 a matsayin sabon albashin, wanda doka ta ce a rika duba shi duk bayan shekara huɗu.
Ganawar tasu na zuwa ne yayin da ƙungiyar ƙananan hukumomi ke neman ɓullo da sabon tsarin ba su kason su na ƙananan hukumomi 774 a faɗin ƙasa,
bayan hukuncin kotun ƙoli da ya tabbatar da ‘yancin kashe kuɗin su da kan su ba tare da sahannun gwamnoni ba.














































