Home Addini A Yau Najeriya Ke Kammala Kwaso Alhazan Ta Daga Sa’udiyya

A Yau Najeriya Ke Kammala Kwaso Alhazan Ta Daga Sa’udiyya

297
0
6A590CC8 E01E 41E0 ABA6 9DA051FD3912
6A590CC8 E01E 41E0 ABA6 9DA051FD3912

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya NAHCON ta ce a yau Talata ce take kammala kwashe mahajjatan daga Kasar Sa’udiyya.

sanarwa da ta bayar ta ce Jimillar mahajjatan jihar Kwara 312 ne za su iso birnin Ilorin a jirgin kamfanin Air Peace.

Ta ce Jirgin nasu shi ne jigila ta 119 kuma ta ƙarshe da suka yi aikin maido da ‘yan Najeriya gida bayan kammala aikin Hajjin na bana.

NAHCON ta ce za ta kammala aikin ne kwana uku kafin cikar wa’adin da ta tsara na kamala aikin kwaso Alhazan.

Jimillar mutum dubu  47 da 171 ne hukumar ta NAHCON ta kai Sa’udiyya cikin kwana 27, sannan ta dawo da Alhazai dubu 50 da 091 cikin kwana 25.

Sai dai a aikin Hajjin na bana Alhazan Najeriya da dama sun yi ƙorafi game da abincin da ake basu yayin zaman su a Sa’udiyyar.

Leave a Reply