Mun Sami labarin rasuwar Muhammad Yabagi Mai shekara 45.
Muhammad Yabagi, ya rasu ne bayan ya yi fama da gajeruwar jinya a Kaduna.
Ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya.
Kafin rasuwarsa Muhammad Yabagi daya ne daga cikin mamba a gammayyar kungiyoyin jam’iyyun siyasar APC
wato Conferedation of All APC support group a Najeriya.
Sannan kuma ‘Kanine ga Prof Kailani Muhammad, wanda shi ne shugaban Kungiyar confederation of APC Group.
Tuni aka yi jana’idarsa a Kaduna kamar yadda addinin musulunci ya tsare,
sai mu yi fatan Allah ya jikanshi da rahama muna Allah ya kyauta karshenmu.