Home Home Atiku Ya Gayyaci Yakubu Shugaban INEC Bada Shaida Kan Shari’ar Tababar Nasarar...

Atiku Ya Gayyaci Yakubu Shugaban INEC Bada Shaida Kan Shari’ar Tababar Nasarar Tinubu

95
0

Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Farfesa Mahmood Yakubu, zai bayyana a gaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Farfesa Yakubu dai zai bada shaida ne a kan ƙarar da Atiku Abubakar ya ya shigar a kan Bola Tinubu da hukumar zabe da jam’iyyar APC, inda ya nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da Bola Tinubu ya yi nasara.

Lauyan Atiku Abubakar Chris Uche ya bayyana wa alƙalan kotun biyar bisa jagorancin Haruna Tsammani cewa, Farfesa Mahmud Yakubu zai bayyana a gaban kotun ranar Alhamis mdin nan.

Lauyoyin Atiku ne su ka gayyaci Mahmud Yakubu tare da aika ma shi sammaci domin ya amsa tambayoyin da za su yi ma shi dangane da jayayyar da Atiku ke yi a kan sakamakon zaɓen.

Leave a Reply