Home Home Tinubu Ya Sanar Da Majalisar Dokoki Aniyar Tura Dakaru Zuwa Nijar

Tinubu Ya Sanar Da Majalisar Dokoki Aniyar Tura Dakaru Zuwa Nijar

38
0

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya shaida wa majalisar dokoki ta tarayya matsayar da ƙungiyar ECOWAS ta cimmawa game da ɗaukar matakin soji a kan Nijar da sauran takunkuman da aka ɗauka na ladabtar da sojojin da su ka yi juyin mulki.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya sanar da saƙon shugaban kasa, inda ya karanto kai tsaye daga wasikar da ya aike masu.

A cikin Wasikar dai, Tinubu ya ce bayan abin takaicin da ya faru a Nijar inda aka hamɓarar da shugaban ƙasa, ECOWAS ta yi Allah-wadai da juyin mulkin, kuma ta amince da ɗaukar matakan dawo da Nijar a kan turbar dimokuraɗiyya.

Ya ce za a rufe dukkan iyakokin Nijar da ƙasashen ECOWAS, tare da sa ido domin tabbatar da cewa an yi biyayya ga matakin.

Ya ce matakan da su ka dauka sun hada da yanke wutar lantarkin da ake kai wa Nijar da neman goyon bayan ƙasashen duniya wajen aiwatar da matsayar ƙungiyar ECOWAS, da kuma datse sufurin jirgin sama daga cikin Nijar da ma wanda zai shiga ƙasar. Sauran sun hada da Rufe hanyoyin shigar da kaya zuwa Nijar daga Legas da kuma wayar da kan ‘yan Nijeriya musamman a

Leave a Reply