Home Labaru Zan Yi Mulkin APC Bisa Adalci – Ganduje

Zan Yi Mulkin APC Bisa Adalci – Ganduje

125
0

Sabon shugaban jami’iyar APC Abdullahi Umar Ganduje, ya
ce zai kama aiki tukuru domin tabbatar da jam’iyyar ta yi
nasara a zaɓen gwamnan jihohin Kogi da Bayelsa da za a
gudanar ranar 11 ga watan Nuwamba.

Ganduje ya bayyana haka ne, lokacin da ya ke jawabi bayan an tabbatar da shi a matsayin shugaban jam’iyyar APC, a wajen taron majalisar zartarwa na jam’iyyar da ya gudana a Abuja.

Haka kuma, an zaɓi tsohon mai magana da yawun Majalisar Dattawa Ajibola Basiru ɗan asalin jihar Osun a matsayin sakataren Jam’iyar APC na kasa.

A jawabin sa, Ganduje ya gode wa Shugaba Bola Tinubu, sannan ya jaddada cewa zai tabbatar da zaman lafiya a cikin jam’iyar.

Leave a Reply