Home Home Sai Kin Nuna Min Ubana —’Ya Ga Uwarta A Kotu

Sai Kin Nuna Min Ubana —’Ya Ga Uwarta A Kotu

29
0

Wata mata ta maka mahaifiyar ta a kotu, ta na neman sai ta nuna mata mahaifin ta a yankin Birnin Tarayya Abuja.

Matar ta ce ta garzaya kotu ne, bayan kannen ta sun matsa cewa dole sai ta fice daga gidan mahaifin su, bisa hujjar cewa ita ba ‘yar cikin sa ba ce.

Yayin zaman kotun, mahaifiyar matar ta gabatar da wani mazaunin unguwar Dutsen Alhaji cewa shi ne tsohon mijin ta, kuma mahaifin ‘yar da ta haifa masa, kafin daga bisani iyayen ta su ka aurar da ita ga sabon mijin ta.

Sai dai mutumin da uwar mai karar ta gabatar ya ce atafau ba ‘yar sa ba ce, domin bai taba kusantar mahaifiyar ta ba ballantana a yi maganar haihuwa a tsakanin su.

Bayan sauraren bangarorin biyu, mai shari’a Abdurrahman Ibrahim ya bada umarnin a yi wa tsofaffin ma’auratan gwajin kwayar halitta, domin tabbatar da ikirarin kowannen su.

Alkalin ya kuma umarce su da cewa su biyun za su biya kudin gwajin da za a yi masu Naira dubu 200, sannan ya dage sauraren shari’ar zuwa ranar 8 ga watan Agusta.

Leave a Reply