Home Labarai Tinubu Ya Amince Da Biyan Kuɗin Kafa Cibiyar Yaɗa Labarai Ta UNESCO

Tinubu Ya Amince Da Biyan Kuɗin Kafa Cibiyar Yaɗa Labarai Ta UNESCO

278
0
Tinubu
Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fitar da kuɗaɗe domin kafa Cibiyar Yaɗa Labarai ta UNESCO wato (Media and Information Literacy Institute, MIL) a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana haka a lokacin wani taro da suka yi da Mataimakin Darakta-Janar na UNESCO, Dakta Tawfik Jelassi, a birnin Paris na ƙasar Faransa.

Muhammad Idris, wanda ya bayyana hakan a gefen ziyarar da Shugaba Tinubu ya kai ƙasar Faransa, ya bayyana irin goyon bayan da Shugaban Ƙasa ke ba aikin.

Ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da goyon baya sosai ga aikin, kuma ya amince da fitar da duk wasu kuɗaɗen da ake buƙata domin cibiyar ta fara aiki nan take, wadda za ta kasance a Babban Birnin Tarayya.

Ministan ya nuna jin daɗin sa ga UNESCO da ta ba Najeriya haƙƙin kafa Cibiyar, wadda ita ce kaɗai irin ta a duniya.

Leave a Reply